17 Satumba 2020 - 09:54
​Kushner: Saudiyya Za Ta Kulla Alaka Da Isra’ila Nan Gaba Kadan

Babban mashawarcin shugaban kasar Amurka Jared Kushner ya bayyana cewa, kasar Saudiyya na daga cikin kasashen larabawa da za su kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, domin su hada karfi wuri guda su tunkari kasar Iran.

ABNA24 : A wata zantawa da ya yi da tashar CNN a jiya Laraba, babban mashawarcin shugaban kasar Amurka Donald Trump kuma surukinsa, Jared Kushner ya bayyana cewa, kasar Saudiyya na daga cikin kasashe 6 da Trump ya ambata kan cewa sunan shirin kulla hulda da Isra’ila nan ba da jimawa ba, domin su yi aiki tare wajen ganin sun tunkari kasar Iran, wadda ya ce ita ce babbar barazana a gare su.

Ya ce a cikin shekaru uku da suka gabata an samu gagarumin canji a kasar Saudiyya tun bayan nada Muhammad Bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, kuma ana ci gaba da ganin tasirin wannan canji, wanda kuma shi ne zai bayar da damar kulla alaka tsakanin kasar ta Saudiyya da kuma Isra’ila.

Shi ma a nasa bangaren shugaban hukumar leken asiri ta Isra’ila Yossi Kohen ya sheda wa tashar talabijin din Isra’ila ta 13 cewa, maganar sanar da kulla alaka tsakanin Isra’ila da Saudiyya maganar lokaci ce kawai, kuma yana sa ran hakan za ta kasance nan da wani dan lokacin kadan.

342/